Babban malamin addini ya yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019

Babban malamin addini ya yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019

Wani babban malamin addinin kirista a Najeriya mai suna Fasto Gabriel Adegboye ya yi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai zarce ba a zaben da za'a yi na shekarar 2019.

Kamar yadda majiyar mu ta jaridar Nigerian tribune ta tuwaito, babban faston ya ayyana cewa ya samu wahayi ne daga ubangijin sa game da cewar wani sabon jini ne zai karbi mulki daga hannun shugaban kasar.

Babban malamin addini ya yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019
Babban malamin addini ya yi hasashen faduwar Buhari a zaben 2019

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo

A wani labarin kuma, Masarautar kasar Saudiyya mun samu labarin cewa sun shiga wata yarjejeniya da mazhabar 'yan addinin kirista ta Vatican domin gina masu coci-coci a dukkan fadin kasar kamar dai yadda gidan yada labaran Beritbart ya ruwaito mana.

Yarjejeriyar kamar yadda muka samu, Sheikh Mohammed bin Abdel Karim Al-Issa ne dake zaman babban Sakataren hadakar kungiyar muslmin duniya ta Muslim World League a turance da kuma Cardinal Jean-Louis Tauran, dake zaman shugaban kungiyar mazhabar kiristocin Vatican suka sa wa hannu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel