Yan Sanda a jihar Enugu sunyi nasarar cire wasu bamabamai da aka binne lokacin yakin Basasa
- Ebere Amarizu, jami’in hukumar ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a ya bayyana cewa anyi nasarar cire bamabaman lafiya lau
- Amarizu ya bayyana cewa hukumar ‘Yan Sandan na jihar Enugu tana sanar da jama’ar kasa cewa aikin da suka gudanar na ciro bamabaman daga ranar 25 zuwa 26 ga watan Afirilu a Enugu anyi nasara
A jawabin da aka gabatar a ranar Alhamis, daga bakin Ebere Amarizu, jami’in hukumar ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a, ya bayyana cewa anyi nasarar cire bamabaman lafiya lau ba tare da wata matsala ba.
Amarizu ya bayyana cewa hukumar ‘Yan Sandan na jihar Enugu tana sanar da jama’ar kasa cewa aikin da suka gudanar na ciro bamabaman daga ranar 25 zuwa 26 ga watan Afirilu na shekarar 2018, a Enugu anyi nasara kuma babu mummunan rahoto game da aikin.
“A lokacin ciro bamabaman, anyi nasarar ciro guda bambaman (UXO) goma sha biyar, wadanda basu tashi ba, a cikin wadanda aka bari a lokacin da ake yakin Basasa, bayan wasu da aka gano a wurin noma, ginin gidaje da kuma hanyoyi, duk anyi nasarar ciresu.
KU KARANTA KUMA: 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)
“Bangaren (E.O.D) na hukumar ‘Yan Sanda a jihar Enugu, ba tare da wani mummuna rahoto ba game da aikin sunce yankin wurin lafiya lau za’a iya gudanar da al’amura ba tare da fargaban komai ba.”
A halin yanzu munji cewayan kunar bakin wake sun sake kai hari Maidauguri.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng