Mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da akayi a hanyar Zamfara

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da akayi a hanyar Zamfara

- Mutane bakwai suka rasa rayukansu a ranar juma’a da aka samu hatsarin mota a hanyar Gusau-Zaria road

- Nasir Ahmed shugaban hukumar kiyaye hadurra, yace hatsarin ya auku ne ta hanyar karo da motocin sukayi gaba da gaba sakamakon mugun gudu da kuma wucewar ganganci da direbobin keyi

- Nasir ya gargadi direbobi musamman na motocin haya dasu siyo na’urar kula da gudun mota wanda ake siyarwa a kasuwa

Mutane bakwai suka rasa rayukansu a ranar juma’a da aka samu hatsarin mota a hanyar Gusau-Zaria road, jami’in hukumar kiyaye hadurra na jihar Zamfara, Nasir Ahmad ya bayyanawa Daily Trust.

Nasir Ahmad shugaban hukumar kiyaye hadurra, yace hatsarin ya auku ne ta hanyar karo da motocin sukayi gaba da gaba sakamakon mugun gudu da kuma wucewar ganganci da direbobin keyi.

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da akayi a hanyar Zamfara
Mutane 7 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da akayi a hanyar Zamfara

Hatsarin ya auku ne bayan kusan sati biyu mutane tara na iyalan gidan dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Bakura, a makamancin hatsarin a kan hanyar Gusau-Sokoto road.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

“A cikin fasinjojin motar 28, 7 sun rasu sai kuma 21 suka samu raunuka. Cikin wadanda suka rasu akwai manya shida sai yaro daya, sai kuma wadanda suka samu rauni suna samun sauki a asibitin Bakura na Specialist”, inji shi.

Nasir ya gargadi direbobi musamman na motocin haya dasu siyo na’urar kula da gudun mota wanda ake siyarwa a kasuwa, wanda zai taimaka wurin rage yawan asarar rayuka da dukiyoyi

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel