Buhari ya dora alhakin lalacewar bangaren lafiya kan gwamnatin Jonathan
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya ya kara jaddada matsayar sa ta cewa tabbas shugabannin kasar Najeriya da suka shude ne musabbabin lalacewar Najeriya duba da yadda ya ce sun mulki kasar.
Haka zalika shugaban kasar wanda mataimakin sa ya wakilta a wajen taron karawa juna ilimi da likitocin Najeriya suka shirya, ya kuma dora alhakin tabarbarewar fannin harkar lafiya kacokan a kan gwamnatin da ta shude ta shugaba Jonathan.
KU KARANTA: An lalata boma-bomai 15 a jihar Enugu
Legit.ng Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa abun takaici ne idan aka yi la'akari da yadda kudin gangar danyen mai ta kai har $100 amma gwamntin baya tayi burus da harkar lafiyar.
A wani labarin kuma, Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a garin Legas a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da da umurnin mallakawa gwamnatin tarayya wasu manyan gidajen alfarma guda biyu mallakin wasu manyan jami'an sojin ruwan Najeriya Kaftin Olotu Morakinyo da kuma Kaftin Ebony Aneke.
Alkalin kotun, mai shari'a Muslim Hassan shine ya yanke wannan hukuncin biyo bayan karar da hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta shigar a gaban sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng