Rikicin manoma da makiyaya ya lakume rayuka 30 a jihar Adamawa
Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su sannan kuma kawo yanzu ba'a ga wasu mutanen ba da dama a wani kazamin rikici da ya barke a tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan.
Kamar dai yadda muka samu, shugaban karamar hukumar ta Numan ya bayyana cewa da wurin karfe 7 na dare ne dai wasu mahara dauke da muggan makamai suka farwa kauyukan karamar hukumar da suka hada da Bolki, Bang da kuma Gon inda kuma suka farwa jama'ar kauyukan tare kuma da kone gidajen su.
KU KARANTA: Dalilin da yasa Yarbawa ba su zabe ni ba a 1999 - Obasanjo
Legit.ng ta samu cewa saidai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa, SP Abubakar Othman ya bayyana cewa mutane 15 ne suka rasa ransu sannan kuma kimanin gidaje 150 aka kone sakamakon rikicin.
Haka ma kuma, Mummunan labarin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa akalla rayuka 13 ne suka rasa rayukan su biyo bayan wani kazamin artabu tsakanin wasu 'yan bindiga makiyaya da kuma 'yan banga a jihar Zamfara.
Kamar dai yadda muka samu duka duka a cikin satin da ya gabata ne wasu 'yan bindigar suka kashe akalla mutane 27 a kauyen Kabaro dake a gundumar yankin Dansadau a karamar hukumar Maru.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng