Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Zamfara

Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Zamfara

Mummunan labarin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa akalla rayuka 13 ne suka rasa rayukan su biyo bayan wani kazamin artabu tsakanin wasu 'yan bindiga makiyaya da kuma 'yan banga a jihar Zamfara.

Kamar dai yadda muka samu duka duka a cikin satin da ya gabata ne wasu 'yan bindigar suka kashe akalla mutane 27 a kauyen Kabaro dake a gundumar yankin Dansadau a karamar hukumar Maru.

Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Zamfara
Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Zamfara

KU KARANTA: Hadakar fatattakar Buhari tayi masa wankin babban bargo

Legit.ng ta samu haka zalika cewa mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Muhammad Shehu ya tabbatar aukuwar lamarin sannan kuma ya bayyana cewa tuni jami'an su sun bazama domin tabbatar da doka da oda.

A wani labarin kuma, Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su sannan kuma kawo yanzu ba'a ga wasu mutanen ba da dama a wani kazamin rikici da ya barke a tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan.

Kamar dai yadda muka samu, shugaban karamar hukumar ta Numan ya bayyana cewa da wurin karfe 7 na dare ne dai wasu mahara dauke da muggan makamai suka farwa kauyukan karamar hukumar da suka hada da Bolki, Bang da kuma Gon inda kuma suka farwa jama'ar kauyukan tare kuma da kone gidajen su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng