Wakilin Borno ya shiga damuwar game da wanda zai maye gurbin Shettima a shekarar 2019

Wakilin Borno ya shiga damuwar game da wanda zai maye gurbin Shettima a shekarar 2019

- Kamar yadda mulkin Shettima a karo na biyu yazo karshe a shekarar 2019, wakilin jihar Borno a majalisa Alhaji Ayuba Mohammed Bello, ya nuna damuwarsa game da wanda zai maye gurbin gwamnan

- Bello wanda ke wakiltar mazabar Jere a karamar majalisa, ya nuna matukar damuwarsa duk da matsalar rashin tsaro dake damun jihar wanda ke dakile cigaban jihar

- Duk da wadannan matsaloli dake damun jihar, amma gwamna Shettima ya taka rawar gani a bangaren ayyukan cigaban jihar

Kamar yadda mulkin Shettima a karo na biyu yazo karshe a shekarar 2019, wakilin jihar Borno a majalisa Alhaji Ayuba Mohammed Bello, a ranar Laraba, ya nuna damuwarsa game da wanda zai maye gurbin gwamnan.

Bello wanda ke wakiltar mazabar Jere a karamar majalisa, ya nuna matukar damuwarsa duk da matsalar rashin tsaro dake damun jihar wanda ke dakile cigaban jihar.

Duk da wadannan matsaloli dake damun jihar, amma gwamna Shettima ya taka rawar gani a bangaren ayyukan cigaban jihar.

Wakilin Borno ya shiga damuwar game da wanda zai maye gurbin Shettima a shekarar 2019
Wakilin Borno ya shiga damuwar game da wanda zai maye gurbin Shettima a shekarar 2019

Bello ya kara da cewa dawowar Sanata Ali Modu Sheriff jam’iyyar APC, ya kawo masa damuwa saboda gudun cewa hakan zai iya kawowa Shettima tangarda game da zaben wanda zai maye gurbinsa don cigaba daga inda ya tsaya ta fannin ayyuka.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da ya sa jaruman Arewa ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba – Fati SU

Saboda haka yake shawartar mutanen jihar dasuyi amfani da wannan damar ta watan Ramadan mai zuwa su roki Ubangiji na “ya zaba masu wanda yafi zama alkhairi, wanda kuma zai cigaba da tafiyar da ayyuka alkhairi wanda gwamnan ya fara aiwatarwa.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da tsohon gwamnan jihar, Ali Modu Sheriff sun yanke shawarar ajiye gabar dake tsakaninsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel