Dalilin dake baiwa Babban sufetan Yansandan Najeriya kwarin gwiwar wulakanta majaisa ya bayyana ƙarara

Dalilin dake baiwa Babban sufetan Yansandan Najeriya kwarin gwiwar wulakanta majaisa ya bayyana ƙarara

Shugaban hadaddiyar kungiyar yayan kabilar Ibo na kasa gabadaya John Nwodo ya bayyana cewar karfin ikon da bangaren zartarwa ke da shi ne yake baiwa babban sufetan Yansandan Najeriya damar rainawa tare da wulakanta majalisun dokokin kasar nan.

Premium Times ta ruwaito Nwodo ya bayyana haka a yayin ziyarar da shuwagabannin kudanci da na tsakiyar Najeriya suka kai ma shugaban majailisar dattawa, Sanata Bukola Saraki a ranar Alhamis 3 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Daga cikin tawagar akwai Olu Falae, Irangate Idongesit, Victor Attah, Stella Omu, Banjo Akintoye, Ayo Adebanjo, Yinka Odumakin, Chukwuemeka Ezeife, Chigozie Ogbu, Ihechukwuma Maduke, Basset Henshaw, Dan Suleiman, Alfred Mulade, Anaba Saraigbe da Maryam Yunusa.

Dalilin dake baiwa Babban sufetan Yansandan Najeriya kwarin gwiwar wulakanta majaisa ya bayyana ƙarara
Buhari, Saraki, Dogara

A yayin ziyarar, majiyar Legit.ng ta ruwaito Mista Nwodo yana cewa tsarin mulkin Najeriya ne ya baiwa bangaren zartarwa wannan karfin iko, don haka shi ne abin dubawa. Kuma ya danganta hakan ga kusten da wasu yan bangan siyasa suka yi cikin majalisa, inda suka duake sandar ikon majalisar, da kuma rashin kunya da Sufetan Yansanda yayi ma majalisar, ta hanyar rashin amsa gayyatar da suka yi masa.

“Mun kawo mana wannan ziyara a matsanancin lokaci a tarihin kasar nan, mun kawo ziyara ga majalisun dokoki ne saboda muhimmin matsayinsu a kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda majalisa ne kadai ke kunshe da dukkanin al’ummar sassan kasar nan.” Inji shi.

Daga karshe Nwodo yayi kira ga shugaban majalisar, Sanata Saraki tare da sauran yan majalisar da su sake duba batun baiwa bangaren zartarwar karfin iko, yace kundin tsarin mulki ne ya basu wannan dama, don haka yace kundin tsarin mulkin kasarnan ya cancan gyara.

A nasa jawabin, Saraki ya tabbatar ma tawagar da suka kai masa ziyara cewar majalisa zata taka rawar da ta kamaceta don tabbatar da dawwamar Najeriya akan tafarkin Dimukadiyya da cigaba mai daurewa, sa’annan ya basu tabbacin majalisa zata sake duba yiwuwar yin garambawul ga kundin tsarin mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel