Tsawa ta hallaka mutane biyu a jihar Kaduna
Anyi wani tsawa a ranar Laraba a jihar Kaduna, inda ya kashe mutane biyu a unguwar sarki dakearewacin Kaduna da kuma karamar hukumar Narayi dake jihar.
Legit.ng ta tattaro cewa wani yaro mai shekaru takwas da aka ambata da suna Baba, na kokarin diban ruwa a wajen gidansu lokacin da wata bishiya ta fado masa sannan ta kashe shi.
A Narayi wani mutun da ba’a san ko wanene ba ya mutu bayan wutan pole ya fado masa ya kuma raba kansa gida biyu.
Baya ga haka iskan rowan ya tuge rufin gidaje da dama da kuma wuraren cinikai, inda ya tuge bishiyoyi da pole din wuta da dama.
KU KARANTA KUMA: Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kaduna, Ben Kure yace bai samu ko wani rahoto ba amma ya shawarci mazauna da su guje ma yawo a karkashin iska mai karfi.
A halin yanzu, Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani yace akwai bukatar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa, wanda zai hada da mutane masu hankali, masu aikin yi da kuma matasa, wanda zai kai Najeriya inda take mafarkin zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng