Yan sandan Najeriya sun lalata wasu muggan boma-bomai 15 a garin Enugu

Yan sandan Najeriya sun lalata wasu muggan boma-bomai 15 a garin Enugu

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Enugu sun bayar da labarin samun nasarar lalata sauran boma-boman da 'yan tawayen yankin Biafra suka yi anfani da su a lokacin yakin basasa har guda 15.

Mai magana da yawun rundunar Sufuritanda Ebere Amaraizu shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ya kuma raba a garin na Enugu.

Yan sandan Najeriya sun lalata wasu muggan boma-bomai 15 a garin Enugu
Yan sandan Najeriya sun lalata wasu muggan boma-bomai 15 a garin Enugu

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Sufuritanda Ebere Amaraizu din ya kuma godewa al'ummar jihar da ma shiyyar baki daya bisa yadda suka nuna halin dattaku da kuma son zaman lafiya yayin lalata makaman.

A wani labarin kuma, Kimanin shekaru 28 da suka shude, Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Mista Boss Mustapha ya yi bayanin yadda yace tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya shirya masa kullalliyar da ta hana shi zama Gwamnan Adamawa.

Kamar dai yadda Boss Mustapha din ya ayyana, biyo bayan sabanin da suka samu da fitaccen dan siyasar Atiku lokacin da ya nemi ya kakaba masa mataimaki, sai kawai ya juya masa baya ya hada kai da jam'iyyar adawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel