Yanzu Yanzu: Buhari ya tsaya a Landan domin a gyara masa jirgi a kuma sha masa mai - Fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari ya tsaya a Landan domin a gyara masa jirgi a kuma sha masa mai - Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ya bayyana dalilan da suka sanya shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya birnin London dake kasar Ingila bayan tafiyarsa zuwa kasar Amurka

- Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa Malam Shehu Garba, yace bayyana cewa jami’an shugaba Buhari sun yanke shawarar tsayawa kasar Inga a kan yanyarsu ta dawowa daga kasar Amruka don su duba lafiyar jirgin kuma su sha mai

- Kamar yadda mai bawa shugaban kasar shawar ta fannin tsaro ya bayyana, yace a yanzu haka shugaban kasar da jai’an nasa sun kan hanyarsu ta dawowa birnin tarayya

Fadar shugaban kasa ya bayyana dalilan da suka sanya shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya birnin London dake kasar Ingila bayan tafiyarsa zuwa kasar Amruka.

Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa Malam Shehu Garba a sakon wayar salula da ya aiko a yau, ya bayyana cewa jami’an shugaba Buhari sun yanke shawarar tsayawa kasar Inga a kan yanyarsu ta dawowa daga kasar Amruka don su duba lafiyar jirgin kuma su sha mai.

Yanzu Yanzu: Buhari ya tsaya a Landan domin a gyara masa jirgi a kuma sha masa mai
Yanzu Yanzu: Buhari ya tsaya a Landan domin a gyara masa jirgi a kuma sha masa mai

KU KARANTA KUMA: An tsige ‘dan Sule Lamido daga sarautar Bamaina, jihar Jigawa

Kamar yadda malam Shehu mai bawa shugaban kasar shawar ta fannin tsaro ya bayyana, yace a yanzu haka shugaban kasar da jai’an nasa sun kan hanyarsu ta dawowa birnin tarayya, “yanzu haka.

“Jirgin karami ne. Babban jirgin yana wurin gyara. Jami’an kula da jirgin sun yanke shawarar yanke doguwar tafiyar, don su shawa jirgin mai su kuma kara duba lafiyarsa. Duk da cewa ba wani abun damuwa bane. Yanzu haka ma suna hanyar dawowa birnin tarayya”, inji shi.

A halin da ake ciki ana sa ran dawowar shugaban kasar gida Najeriya a yammacin yau Alhamis.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng