Ai kaji irinta: Halin sata ya sa kotu ta raba Miji da Mata bayan shekaru biyu da aure

Ai kaji irinta: Halin sata ya sa kotu ta raba Miji da Mata bayan shekaru biyu da aure

- Mummunan halaye kan zama cikas ga zamantakewar aure, kamar yadda ya zama hakan tsakanin ma'auratan da alkali ya raba su

- Magidancin dai ya koka da halin beran da matarsa ke yi da kuma binceke masa aljihunansa da zarar ya cire kaya

Yanzu haka dai wata kotu dake Mapo a Ibadan ta raba auren wasu ma'aurata duk kuwa da cewa sun shafe shekaru har biyu da aure.

Raba auren ya biyo bayan rokon da mijin matar mai suna Fatima ya shigar gaban kotun, yana rokonta da ta taimaka ta sauwake mashi don halin da matar tasa ke yi na sace-sace da dauke-dauke barazana ne ga tattalin arzikinsa da ma rayuwarsa baki daya.

Ai kaji irinta: Halin sata ya sa kotu ta raba aurensu bayan shekaru biyu da aure
Ai kaji irinta: Halin sata ya sa kotu ta raba aurensu bayan shekaru biyu da aure
Asali: UGC

Akeem wanda shi ne mijin matar, ya ce, yayi-yayi da matar tasa ta tuba amma halin beran nata da dabi'ar caje aljihunsa da zarar ya cire kaya kamar ma karuwa take, a don haka ne ya ke so kotun ta tabbatar da rabuwarsu domin kowa ya kama gabansa.

"Duk sati ina bata kudin cefane har sama da N2,000 duk kuwa da cewa akwai kayan abinci mai yawa a gida na." inji mijin Fatima.

ya ce, "Amma da zarar ya fita daga gida, sai matar tasa ta shi lalube masa aljihu ta kwashe kudadensa."

Alkalin kotun mai shari'a Ademola Odunade, ya ce, tabbas halin dauke-dauke ba dabi'a ce mai kyau ba, kuma Shari'a tayi Allah wadai da ita. A don haka, ya amince da rabuwar auren nasu domin samuwar kwanciyar hankali ba tare da an cutar da wani ba.

KU KARANTA: Najeriya za ta ciri tuta a bangaren takin zamani a 2018 – Dangote

Amma kuma alkalin yace, duba da jaririn da yake tsakanin ma'auratan dan wata takwas, kotun ta umarci Akeem da ya rika biyan Naira N5,000 kudin ciyar da dan nasa sannan kuma zai dauki nauyin iliminsa da walwalarsa.

Ana ta bangaren, Fatima wadda malamar makaranta ce, cewa tayi, duk sharri mijin nata yake yi mata. Kuma mijin nata ya kuntatawa rayuwarta tun bayan da tayi haihuwar farko.

"Har ma ya taba fada min cewa shi fa ya gaji da zaman aurenmu, sai ya daina suke duk nauye-nauyen da suka rataya a wuyansa, duk kuwa da yasan ban murmurewa daga fidar da aka yi min ba a dalilin haihuwar dansa ba." wannan ne dalilin da yasa har na kutsa dakinsa domin samun abinda zan dauka na siyar don samun kudin cin abinci da sauran bukatu na.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng