Tambaya: Buhari ya bar Amurka ranan Talata amma har yanzu bai dawo Najeriya ba, ina yaje?
Har yanzu babu wanda ya san inda shugaba Muhammadu Buhari ya shiga, kwanaki biyu bayan barinsa filin jirgin Washington inda ya gana da shugaban kasan Amurka, Donald Trump.
Da Najeriya ya taho, da tun jiya Laraba ya iso Najeriya amma har yau Alhamis babu labarinshi.
Jirgin shugaban kasa, Eagle One, ya bar filin jirgin saman Joint Base Andrews da safiyar Talata kuma ya isa Landan karfe 9:42 na dare bisa ga na’urar Flight radar 24 wacce ke bibiyan jiragen duniya.
Amma har karfe 10 na safiyar Alhamis, jirgin na Landan kuma babu wani bayani daga masu Magana da yawunsa.
Jawabin masu Magana da yawin shugaban kasa bai nuna cewa bayan Buhari ya bar Amurka zai biya Landan ba tunda y agama halartan taron Commonwealth da ya kaishi Landan.
KU KARANTA: Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka
Jaridar PREMIUM TIMES ta kira masu Magana da yawunsa, Femi Adesina da Garba Shehu domin tambayarsu amma basu amsa wayoyinsu ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng