Boko Haram: Masu bayar da agaji sun sada uwa da diyarta bayan shekaru 4 da rabuwarsu

Boko Haram: Masu bayar da agaji sun sada uwa da diyarta bayan shekaru 4 da rabuwarsu

- Kwamitin bayar d taimako na duniya a ranar Laraba ta bayyana cewa ta sake sadar da Aishatu Shehu da diyarta mai shekaru 7, Amina, bayan shekaru 4 da rabuwarsu sakamakon rikicin Boko Haram

- Pamela Ongoma daya daga cikin jami’an na ICRC ta bayyana cewa sun hada uwar da diyarta bayan bincike da sukaita gudanarwa ta hanyar wayar salula, musayar hotuna da wasu hanyoyi da dama

- Ongoma tace Amina ta rabu da mahaifiyarta tun shekarar 2014, lokacin tana ‘yar shekara 3, bayan ‘yan Boko Haram sun kai hari a kauyensu na karamar hukumar Askira Uba

Kwamitin bayar d taimako na duniya a ranar Laraba ta bayyana cewa ta sake sadar da Aishatu Shehu da diyarta mai shekaru 7, Amina, bayan shekaru 4 da rabuwarsu sakamakon rikicin Boko Haram.

Pamela Ongoma daya daga cikin jami’an na ICRC ta bayyanawa manema labarai a garin Adamawa a ranar Laraba, cewa sun hada uwar da diyarta bayan bincike da sukaita gudanarwa ta hanyar wayar salula, musayar hotuna da wasu hanyoyi da dama.

Boko Haram: Masu bayar da agaji sun sada uwa da diyarta bayan shekaru 4 da rabuwarsu
Boko Haram: Masu bayar da agaji sun sada uwa da diyarta bayan shekaru 4 da rabuwarsu

Ongoma tace Amina ta rabu da mahaifiyarta tun shekarar 2014, lokacin tana ‘yar shekara 3, bayan ‘yan Boko Haram sun kai hari a kauyensu na karamar hukumar Askira Uba dake jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka

Ongoma tace an gano Aishatu a karamar hukumar Maiha dake Adamawa sai kuma Amina diyar tata an ganota ne a hannun uwar dakin data dauketa a kauyen Dusulu na karamar hukumar Damboa dake Borno a shekarar 2017.

NAN ta ruwaito cewa kusan iyalai 23 ne suke sake haduwa da danginsu a yankin arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2016 bayan rabuwarsu sakamakon rikicin Boko Haram.

A farkon makon nan muka ji cewa wasu yan kunar bakin wake biyu sun kai hari wani masallaci dake kasuwar Mubi na jihar Adamawa, wanda yayi sanadiyan mutuwar wasu da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel