Naka shi ke bada kai: An fallasa wadanda suka dasa bam a gidan shugaban Inyamuran Najeriya

Naka shi ke bada kai: An fallasa wadanda suka dasa bam a gidan shugaban Inyamuran Najeriya

Tsohon sakataren hadaddiyar kungiyar Inyamuran Najeriya, Ohanaeze Ngigbo, Cif Nduka Eya ya fallasa mutanen da suka dasa wani bam da ya tashi a gidan shugaban Kungiyar mai ci a yanzu, Cif Nnia Nwodo, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nduka yana cewa wannan ba aikin kowa bane face wasu Matasan Inyamurai marasa kunya da basu san girman na gaba dasu ba, ya kara da cewa tashin bom din ya nuna matsayin da tabarbarewar tsaro ta kai a Najeriya.

KU KARANTA: Hauwa Maina ta rasu, karanta wasu muhimman bayanai game da ita guda 8 da baka sani ba

Naka shi ke bada kai: An fallasa wadanda suka dasa bam a gidan shugaban Inyamuran Najeriya
Tashin bom

Bugu da kari, Nduka ya daura alhakin kai harin ga wasu matasan kabilar Ibo, wanda yace suna kokarin hambarar da shugabancin Nwodo, domin su samu damar aiwatar da wasu munanan manufofi a kasar Inyamurai.

A cewar Nduka: “Dama a baya wasu yan matasan Ibo marasa kunya sun sanar da cewar sun kawar da Nwodo a matsayin shugaban Ohanaeze, wannan babban laifi ne a kasar Ibo, ta yaya zaka cire mutumin da baka zaba ba.?”

Naka shi ke bada kai: An fallasa wadanda suka dasa bam a gidan shugaban Inyamuran Najeriya
Ziyarar Kwamishinan

A ranar Lahadin data gabata ne aka jiyo tashin wani Bom a gidan Nwodo dake unguwar Ukehe, jihar Enugu misalin karfe 9 na safe, inda aka hangi wani mutum ya jefa bom cikin gidan ta samar Katanga daga waje.

Sai dai Kwamishinan Yansandan jihar ya bayyana bom din a matsayin karamin alhaki, amma tace ya ragargaza winduna guda biyu na wani daki, a yayin da ya kai ziyarar gani da ido gidan, inda ya bukaci mazauna unguwar da su bude idanuwansu su lura da masu zirga zirga a unguwar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel