Ko Kidahumi ya san Buhari ya gaza - Obasanjo

Ko Kidahumi ya san Buhari ya gaza - Obasanjo

- Ko sakarai ya san Buhari ya gaza, Obasanjo ya sake sakin sabuwa

- Tsohon shugaban kasan ya goyi bayan BUhari a 2015 amma ya ce ba zai sake hakan ba

Kuma dai, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya sake harbin shugaba Muhammadu Buhari da wutan aradu.

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Aremu Obasanjo, ya sake sukan shugaba Buhari inda yac eko sakaran mutum ba zai yabi wannan gwamnati ba.

Obasanjo ya bayyana hakan yayinda yake karyata wasu rahotanni da ke cewa yana marawa tazarcen Buhari baya.

Tsohon shugaban ya jaddada cewa tuni shi ya bayyana matsayarsa ga Buhari a wasikar d aya rubuta a watan Junairun 2018.

Ko Kidahumi ya san Buhari ya gaza - Obasanjo
Ko Kidahumi ya san Buhari ya gaza - Obasanjo

A wasikar da ya rubuta a Junairu, Obasanjo ya bukaci shugaba Buhari da ya ajiye niyyar sake takara saboda yan Najeriya sun sha bakar wahala a gwamnatinsa.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi, ya saki, Obasanjo ya zargi magoya bayan Buhari da yada rashin gaskiya cikin jama'a akanshi.

KU KARANTA: Yan bangan siyasa sun kai ma wani na hannun daman gwamnan jihar Kebbi farmaki

Yace: "Yan Najeriya sun san Obasanjo da fadin gaskiya akan talaucin da yayi katutu a kawunan mutane, rashin jituwan da juna, sanadiyar rashin iyawan shugaba Buhari.

Wannan gazawa na shugaba Buhari ba zai taba siffantuwa da kokari ba, ko sakarkaru sun sani ballanta Obasanjo."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel