Tsaro: Yan sanda sun damke yan kungiyar asiri da yan fashi da makami 25 da bindigu masu yawa

Tsaro: Yan sanda sun damke yan kungiyar asiri da yan fashi da makami 25 da bindigu masu yawa

- Dubun wasu matasa masu aika laifi iri-iri ta cika, bayan da yan sanda suka kai musu kamun kazar kuku

- Matasan da yawancinsu dalibai ne sun shiga hannu har ma sun fara bayani

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Enugu, tayi ram da wasu da ake zargin yan kungiyar asiri ne da kuma yan fashi da makami su 25, a ranar Litinin din da ta gabata da misalin 1:00 na dare, yayin wani taron mambobinsu a jihar.

Yan sandan kuma sunyi nasarar kame bindigunsu da harsasai tare kuma da wasu muggan makamai da ake kerawa a nan cikin gida.

Tsaro: Yan sanda sun damke yan kungiyar asiri da yan fashi da makami 25 da bindigu masu yawa
Tsaro: Yan sanda sun damke yan kungiyar asiri da yan fashi da makami 25 da bindigu masu yawa

Mai magana da yawun rundunar yan sanda na yankin SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana hakan, ya kuma kara da, sun yi nasarar kama su ne a wani kasurgumin daji dake kewayen birnin jihar ta Enugu.

KU KARANTA: Kungiyar tsagerun Niger Delta ta bawa gwamnati kwanaki 14 ko ta fara barin Ala-tsine

Amaraizu ya ce, sashin yaki da yan kungiyar asiri ne na rundunar da kuma taimakon bayanan sirri yasa akai nasarar damke wadanda ake zargin.

"Mun samu bayanai da suke nuna cewa, wasu dalibai daga makarantu da dama da yawansu ya kai 25 suna taron mambobinsu na kungiyar Black Axe Ayes confraternity a dajin Obeagu-Amechi Awkunanaw."

kuma bayan nasarar da suka samu na cafke wadanda ake zargin, sun taimaka kwarai wurin bayar da bayanai ga hukumar yan sandan a cewar kakakin yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel