Sayan wayyar hannu na iya jefaka cikin Kurkuku – Hukumar RRS

Sayan wayyar hannu na iya jefaka cikin Kurkuku – Hukumar RRS

Garin neman gira, za'a rasa ido. Yan Najeriya sun shahara da sayan wayoyin hannu saboda neman sauki. Alhali Wadannan wayoyi da aka fi sani da 'UK used ko Second hand' yawanci na sata ko na yan Damfara.

Kwamandan hukumar Rapid Response Service (RRS), Tunji Disu, ya bayyanawa yan Najeriya cewa sayan wayan hannu wadanda aka fi sani da ‘UK used’ na iya jefa mutum cikin kurkuku idan ya fita daga Najeriya.

Sayan wayyar hannu na iya jefaka cikin Kurkuku – Hukumar RRS
Sayan wayyar hannu na iya jefaka cikin Kurkuku – Hukumar RRS

Disu ya bayyana cewa yawancin wadannan wayoyi anyi amfani da su wajen ayyukan zamba a kasashen waje sannan aka shigo dasu Najeriya musamman jihar Legas.

Yace: “Za ka iya shiga kurkuku idan ka tafi da wayan hannun da ka saya kasar Ingila, Amurka, Jamus, Afrika ta Kudu da sauransu saboda yawancin wayoyin nan, an yi amfani da su wajen aikata ayyukan zamba ko kuma sata. Mun samu irin wadannan wayoyi a jihar Legas. Ayi hattara".

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng