Ramadan: Malami ya gargadi ‘yan kasuwa game da kara kudin kayayyaki

Ramadan: Malami ya gargadi ‘yan kasuwa game da kara kudin kayayyaki

- Daya daga cikin malaman addinin musulunci Alhaji Abdulraheem Jimoh yayi kira ga ‘yan kasuwa da kada su karawa kayayyakinsu kudi gabanin zuwan watan Ramadan

- Jimoh yace ya zamanto al’adar ‘yan kasuwa da daman a karawa kayayyakin da zarar watan Ramadan ya gabato

- Yace yana da muhimmanci ga wadannan ‘yan kasuwa musamman musulman cikinsu, su san cewa watan Ramadan wata ne da ake bukatar ka bayar da sadaka don samun lada

Daya daga cikin malaman addinin musulunci Alhaji Abdulraheem Jimoh yayi kira ga ‘yan kasuwa da kada su karawa kayayyakinsu kudi gabanin zuwan watan Ramadan.

Jimoh wanda ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai na NAN a ranar Laraba a garin Ilorin, yace ya zamanto al’adar ‘yan kasuwa da daman a karawa kayayyakin da zarar watan Ramadan ya karato.

Ramadan: Malami ya gargadi ‘yan kasuwa game da kara kudin kayayyaki
Ramadan: Malami ya gargadi ‘yan kasuwa game da kara kudin kayayyaki

Yace yana da muhimmanci ga wadannan ‘yan kasuwa musamman musulman cikinsu, su san cewa watan “Ramadan wata ne da ake bukatar ka bayar da sadaka don samun lada.”

KU KARANTA KUMA: Miji ya kashe matarsa saboda taki yi masa wankin kayansa Miji ya kashe matarsa saboda taki yi masa wankin kayansa

Ya kara da cewa mutane su kasance masu yin ayyukan da zasu sanya su samu lada, su rabu da wadanda ke kokarin tayar da fushin Allah.

Ramadan ana tsammanin farashi ko 15 ga watan Mayu ko 16 ga watan Mayu, a yanda malaman addinin musulunci suka bayyana.

Idan zaku tuna a ranar Juma'a ne sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad ya sanar da ranar 27 ga watan Mayu a farkon Ramadana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel