Babu yarjejeniyar da nayi da Donald Trump, tattaunawa kawai muka yi - Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin cewa babu wani yarjejeniyar da yayi da shugaba kasan Amurka, Donald Trump, yayin ganawarsu a fadar shugaban kasan na White inda ya amsa goron gayyatarsa.
Shugaba Buhari ya gana Da na Amurka Donald Trump ne ranan Litinin, 30 ga watan Afrilu inda suka tattauna kan al’amura daban-daban da ya shafi kasashen guda biyu.
Yayinda yake ansa tambayoyi a wani hira da yayi sashen Hausa muryar Amurk VOA ranan Talata, Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa da abubuwan da aka fadawa shugaban kasan Amurka kan kashe-kashen da ke faruwa a Najeriya.

Yayinda aka tambayeshi cewa shin ya yi wasu yarjejeniya da Trumo, yace: “Babu yarjejniya, tattaunawa kawai mukayi. Na farko shine labarin da aka bas u (Amurkawa) cewa Kiristoci ake kashewa a Najeriya, kuma abinda ya faru a coci ai ya faru da yankun Kudu maso gabas amma da ya faru a Arewa, sai suka ce Makiyaya ke kashesu.”
“Wadanda suka wadannan maganganu kan makiyaya sun sani kwarai cewa sanduna kawai suke rikewa, rike bindiga wani bakon abu ne. Kuma masu zargin sun sani cewa rikici makiyaya da manoma tsohon abu ne tun kafin a haifemu.”
Shugaba Buhar ya dawo Najeriya bayan ziyarar kwana biyu da ya kai Amurka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng