Babu gudu babu ja da baya akan mafi karancin albashi ya kasance N66,500 - NLC, TUC
- Kungiyar NLC tace zata jurewa yunkurin gwamnati na rage bukatarsu ta mafi karancin albashi a kasar nan ya zama N66,500
- Shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya bayyana hakan wurin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2018 a birnin tarayya
- Mista Ayuba yace Karin da ake bukatar ayi na albashin ma’aikata, shine don su daidaita da cigaban tattalin arziki na wannan zamanin a kasar nan
Kungiyar NLC tace zata jurewa yunkurin gwamnati na rage bukatarsu ta mafi karancin albashi a kasar nan ya zama N66,500.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya bayyana hakan wurin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2018 a ranar Talata, a birnin tarayya.
Bikin ranar ma’ikatan anyi masa take da “Labour Movement in National Development: Dare to Struggle, Dare to Win.”
Wabba yace “ Daga mafi karancin albashi shine N125 wanda yayi daidai da $200, a shekarar 1981 zuwa mafi karancin albashi a yanzu shine N18,000, ma’aikatan Najeriya a ko yaushe ana matsa masu dasu rage bukatarsu a duk lokacin da suka nemi kari."
Bayan haka duk jiran da ake sasu sunayi a karshe dan abunda za’a kara masu kalilan ne, wanda bai kaiga tarada da cigaban da ake samu a kasar ta Najeriya ba.
Mista Ayuba yace Karin da ake bukatar ayi na albashin ma’aikata, shine don su daidaita da cigaban tattalin arziki na wannan zamanin a kasar nan.
KU KARANTA KUMA: Tsaraba 5 da shugaba Buhari ya dawowa yan Najeriya da su daga Amurka
Shugaban kungiyar ULC Joe Ajaero a jiya ya bukaci gwamnati da tayi amfani da bukatarsu ta mafi karancin albashi ya zama N96,000, a matsayin dabarar cin zabe a shekarar 2019. Yace suma tasu kungiyar zata jurewa duk wani yunkuri na da gwamnatin zatayi na hanasu bukatarsu.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Gombe, Ibarahim Dankwanbo yace a shirye suke da biyan naira 66,500 a matsayin mafi karancin albashi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng