Shugaban kasa ya fallasa kudurin tsohon shugaba Jonathan na korar ma'aikata

Shugaban kasa ya fallasa kudurin tsohon shugaba Jonathan na korar ma'aikata

Fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Talatar da ta gabata da yayi daidai da ranar ma'aikata a dukkan fadin Najeriya ta fallasa wani abu da ta kira kullalliyar da gwamnatin shugaba Jonathan ta shirya yi na korar ma'aikata da dama.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata makala da maitaimakawa shugaban kasar na musamman kar harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar inda ya ce tuni har shire-shiren dabbaka hakan yayi nisa kafin Allah ya kawo gwamnatin Buhari.

Shugaban kasa ya fallasa kudurin tsohon shugaba Jonathan na korar ma'aikata
Shugaban kasa ya fallasa kudurin tsohon shugaba Jonathan na korar ma'aikata
Asali: Twitter

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne kuma sai ya ayyana cewa wannan ne ma ya sa daya daga cikin matakan da shugaba Buhari ya fara dauka bayan hawan sa karagar mulki shine na dakatar da shirin korar ma'aikatan.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wata tattaunawa da yayi da gidan yada labarai na Muryar Amurka ya dora alhakin tabarbarewar harkoki a kasar Najeriya kacokam a kan tsaffin shugabannin kasar.

Haka zalika shigaban ya kuma kara yin haske game da kalaman sa akan matasa da suka yi ta jawo cece-kuce kimanin makwonni biyu da suka shude inda yace 'yan jarida ne suka jirkita maganar ta sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng