Kalli hoton mace ta farko dake tuka jirgin sama daga jihar Katsina
Babu shakka matan Najeriya sun zamo masu nasara ta fannin habbaka masana’antu daban daban da tattalin arzikin kasar.
A daidai lokacin da matan arewa sukayi kaurin suna wajen zamowa matan aure na din-din-din, Ruqayya Suleiman ta yanke shawarar canza wannan hasashe akanta.
A yanzu haka Ruqayya ta shiga layin da maza suka fi suna wato aikin tukin jirgin sama wanda hakan ya burge mutane da dama.
An bayyana Ruqayya a matsayin mace ta farko matukiyar jirgin sama daga jihar Katsina, ana taya ta farin ciki ne kamar yadda yau ya zamo ranar ma’aikata.
KU KARANTA KUMA: Ana tsammanin majalisar zartarwa zata saki kasafin kudi na shekarar 2018 a ranar Alhamis
Hakan ya zamo abun alfahari ga mutanen arewa musamman yadda ake yiwa matan yankin kallon karazube.
A kwanan nan ne dai matasan Najeriya suka dunga tada jijiyoyin wuya akan furucin da aka danganta da shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa matasan kasar cima zaune ne.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng