Mara gaskiya ko a ruwa gumi yake: Sojojin Najeriya sun damke barayin danyan mai tare da komatsansu
- Sojojin ruwa sunyi hubbasa a yammacin Najeriya
- Dubun barayin dayen man ta cika bayan sunyi kicibis da sojojin sintirin
- Rundunar Sojin ruwan ta kuma sada barayin ga hukumar yan sanda domin cigaba da bincike
Rundunar Sojin ruwa ta kasa ta mika wadansu mutane su 32 da ake zargin barayin danyan mai ne tare da kayayyakinsu ga hukumar yan sanda a yankin Okitipupa.
Shugaban Sojojin sintiri na yankin Igbokoda, Kaftin Sabo Lengaya, ne ya tabbatar da hakan a jiya Litinin a Lagos.
Lengaya ya ce, rundunar tasu ta mika jarkoki masu cin lita 30 har guda 370 dauke da danyan man, tare kuma da ruwan kudi da yakai N1,199,000 da motoci guda 13 da kuma wayoyin hannu na wadanda ake zargin.
KU KARANTA: Jami’an hukumar Kwastam zasu samu karin albashi mai tsoka nan gaba kadan – Hamid Ali
Kaftin din ya ce, “Sojojin na tsaka da sintiri ne, su kayi arangama da jerin gwanon motocin wadanda ake zargin a kan hanyar tafiya Igbokoda-Okitipupa ta jihar Onda, bayan caje motocin ne kuma suka gano suna dauke ne da haramtaccen tacaccen man.”
"Koda muka zurfafa bincike ne, sai muka gano cewa kayan an dauko su ne daga cikin dokar daji a cikin kwale-kwale a Ugbonla, kuma jarakunan ma can za’a kaisu domin zuba musu.”
“Duk wani yunkurin café masu dauke da jarakunan yaci tura, sakamakon tserewa da sukai da suka hango sojojin” Kaftin din sojan ya shaida
Sannan ya kara da cewa, kayan da aka kama din ba su da takardun sahalewa. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng