Kai co: Allah ya jefawa kasar Isra'ila mugun bala'in zaizaiyar kasa
Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, yanzu haka kasar Isra'ila ta Yahudawa dake a gabas ta tsakiya na cikin halin ha'ulai biyo bayan mmuguwar zaizaiyar kasa da ta kunno kai a kudancin kasar Isra'ila wadda ta yi sanadiyyar tsunduma al’umar kasar cikin halin ni ‘yasu.
Yanzu haka dai mun samu cewa kwanaki akalla 4 kenan da ibtila'in zaizaiyar kasa ta far wa kudanci kasar wanda ya janyo tsayuwar lamurra cak.
KU KARANTA: Mafi karancin albashin Naira dubu 18 abun kunya ne - Atiku
Legit.ng ta samu cewa annobar dai ta yi sanadiyyar ajalin akalla dalibai 10 daga cikin 25 da ke tafiya a cikin wata motar bas da lamarin ya rutsa da su.
A wani labarin kuma, Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan wani mutum da ya yi ridda tare da yin kalaman batanci ga Annabi.
Hankalin hukuma ya kai kan Ahmad Al-Shamri a shekarar 2014 bayan ya saka wasu faifan bidiyo dake nuna akidar mulhidanci a dandalin sada zumunta. An gurfanar da shi gaban kotu bisa tuhumar sa da batanci da kuma mulhidanci tare da yanke masa hukuncin kisa a shekarar 2015.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng