"Ya ga jami'an 'yan sanda na anfani da motar sa da aka sace shekaru 2 da suka wuce"
Wani matashi mai akalla shekaru 32 a duniya dan kasar Ghana dake aiki a wani banki ya ankarar da jama'a yadda ya ga jami'an 'yan sandan kasar na anfani da motar sa da 'yan fashi suka kwace masa tare da kusan halakashi shekaru kimanin biyu da suka shude.
Matashin mai suna Samuel Forson ya ayyana cewa a shekarar 2015 ne dai wasu 'yan fashin da ba'a san ko suwaye ba suka tare shi suka kuma kwace masa kwamfutar sa da motar sa.
KU KARANTA: Dalilin da yasa Oyegun janye kudurin sa na sake tsayawa takara a APC
Legit.ng ta samu cewa ya zuwa yanzu dai ba mu kai ga samun martani daga hukumomin 'yan sandan kasar ba game da batun dake cigaba da daukar hankali.
A wani labarin kuma, Dan tsohon gwamnan daya daga cikin jihohin Najeriya na shiyyara kudu maso yammacin Najeriya ya gurfana a gaban kotun majistare ta garin Legas bisa zargin sa da almundahana ta makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 40.
Dan tsohon gwamnan mai shekaru akalla 40 a duniya, kamar yadda muka samu sunan sa Akinkunle Olunloyo kuma yana sana'ar gudanar da gidan rawa ne kuma 'yan sandan Najeriya ne suka gurfanar da shi a gaban kotun.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng