Maganar tsige Buhari tun farkonta ta mutu - Ndume

Maganar tsige Buhari tun farkonta ta mutu - Ndume

- Tsohon shugaban majalisa Ali Ndume (APC, Borno) ya kalubalanci yunkurin abokan aikinsa game da tsige Buhari daga kujerarsa

- Sanata Mathew Urhoghide (PDP, Edo) ya kawo shawarar a tsige shugaba Buhari daga kan kujerarsa a ranar Alhamis data gabata, wanda ya kawo hujja daga sashe na 143 na dokar kasa ta shekarar 1999

- Urhoghide ya samu goyon bayan wasu sanatoci, Chukwuka Utazi (PDP, Enugu), da kuma Sam Anyanwu (PDP, Imo) wadanda sukace a fara shirye shiryen tsigeshi daga kan mulki

Tsohon shugaban majalisa Ali Ndume (APC, Borno) ya kalubalanci yunkurin abokan aikinsa game da tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerarsa ta shugabancin kasar Najeriya.

Sanata Mathew Urhoghide (PDP, Edo) ya kawo shawarar a tsige shugaba Buhari daga kan kujerarsa a ranar Alhamis data gabata, wanda ya kawo hujja daga sashe na 143 na dokar kasa ta shekarar 1999.

Urhoghide ya kawo shawarar tsige shugaba Buhari ne akan ya cire $496m daga asusun gwamnati don siyen jiragen yaki daga kasar Amruka ba tare da izinin majalisa ba.

Urhoghide ya samu goyon bayan wasu sanatoci, Chukwuka Utazi (PDP, Enugu), da kuma Sam Anyanwu (PDP, Imo) wadanda sukace a fara shirye shiryen tsigeshi daga kan mulki.

Maganar tsige Buhari tun farkonta ta mutu - Ndume
Maganar tsige Buhari tun farkonta ta mutu - Ndume

Ndume yace yunkurin nasu bazai taba tabbata ba saboda dalilai guda uku: “na farko, Buhari yayi wannan hukunci ne bisa kwararan dalilai. Lokuta da dama anyi kokarin sayen jiragen amma abun bai yiwu ba saboda zargin cin zarafin dan adam da akeyi.

“Zuwan Buhari saboda gaskiyarsa kasar Amruka ta amince mana da biyan kudin jiragen yakin. Shugaban kasar ya biya kudin ne da kansa ba ta hannun dan kwagila ba.” Inji shi.

Yace “na biyu shine dokar kasa ta shekarar 1999 sashe na 82 ta bashi damar cire kudin ba tare da izinin majalisar ba.

KU KARANTA KUMA: MSSN tayi Allah wadai da jawabin Trump game da kisan kiristoci a Najeriya

“Na uku, shine tun shekarar 1999 babu wani lokaci da aka cire kudi daga asusun ajiya na ribar danyen mai tare da izinin majalisa, kuma bayan haka wannan abu tun gwamnatin baya ta farashi. Kuma shugaban kasar yace a sanshi cikin kasafin kudi na shekarar 2018 kuma gashi a gaban mu."

Idan dai zaku tuna a makon da ya gabata Legit.ng ta kawo cewa wasu sanatoci sunyi kira ga tsige shugaba Buhari saboda cire kudin siyan jirgi da yayi ba tare da izinin majalisa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng