Boko Haram: Yayinda Buhari ya je ganawa da Trump, sabbin jiragen yaki Mi-35M guda biyu sun shigo Najeriya

Boko Haram: Yayinda Buhari ya je ganawa da Trump, sabbin jiragen yaki Mi-35M guda biyu sun shigo Najeriya

Hukumar sojin saman Najeriya a yau Litinin 30 ga watan Afrilu, 2018 ta karbi sabbin jirage masu saukan angulu Mi-35M wanda gwamnatin Najeriya ta saya daga hannun kasar Rasha.

Jirgin Antonoy wanda ya kawo jiragen ya sauka a barikin sojin saman Makurdi misalin karfe 12:20 na rana. Shugaba injiniyoyin hukumar, Abdulganiyu Olabisi, ya karbi jiragen a madadin babban hafsan sojin, Sadique Abubakar.

Kana wasu jami’an sojin saman kasar Rasha sun rako jiragen domin taimakawa wajen hada jirgin saboda a rarrabe aka kawo su. Kana jami’an hukumar Kwastam da shiga da fice sun rako jirage.

Wadannan sabbin jiragen sabbi ne kuma ana iya amfani da su wajen yaki da daddare. Yana dga cikin jirage mafi kyawu.

Boko Haram: Yayinda Buhari ya je ganawa da Trump, sabbin jiragen yaki Mi-35M guda biyu sun shigo Najeriya
Jirgin da aka sayo

Wannan shine karo na biyu da da hukumar sojin saman Najeriya zasu karbi irin wadanan jiragen tun lokacin shugaba Buhari ya bada umurnin sayo su a 2015.

KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa guda 32 dauke da man fetir da kayan abinci na gab da isowa Najeriya

Hukumar ta karbi na farko a watan Disamban 2016 inda akayi amfani dasu wajen yaki da ta’addanci. Kana kuma an tura wasu jami’an hukumar kasar Rasha domin horo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel