Gyaran ilimi: Gwamnatin tarayya ta saki N138b don gyaran ilimi tun daga tushe
- An kaddamar da shirin da zai gano yawan Malamai da dilibai da kuma abinda ilimi yake bukata don saukin magancewa
- Gwamnatin tarayya ce tayi hubbasar domin gyaran ilimi a fadin kasar nan
- Ministan ilimi na kasa ne ya shaida hakan a wajen wani taro
Gwanatin tarayya ta ce, ta saki zunzurutin kudin da ya wuce Naira biliyan N138b a shekaru uku da suka gabata domin cigaban sashin ilimi a fadin kasar nan.
Ministan ilimi na kasa Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da tsarin tantance ma’aikata na kasa (NPA) na ilimin bai daya a babban birnin tarayya Abuja.
Malam Adamu ya ce, kudin na karkashin kulawar hukumar ilimin bai daya ne kuma jahohi sun samu damar amfanuwa da su har ma da babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa guda 32 dauke da man fetir da kayan abinci na gab da isowa Najeriya
Ya kuma cigaba da cewa, “Tun da aka kafa hukumar ilimin bai dayan a shekarar 1999, sau biyu ne kacal aka taba aiwatar da tantancewar ta kasa baki daya, a shekarar 2006 da kuma 2010. Kuma tantancewar da aka gudanar tafi mayar da hankali ne kawai ga makarantun gwamnati banda masu zaman kansu.”
Sannan ya bayyana cewa, za’a kafa gidauniya mai karfi don samun kwarewa wajen amfani da fasahar sadarwa domin gudanar da aikinsu, domin habakawa gami da shigar da kimiyya cikin aiyukan hukumar ilimin bai dayan, don kawo cigaba a fannin tafiyar da harkokin ilimi.
Sakataren hukumar ilimin bai daya ta kasa, Dr Hamid Bobboyi ya ce, rashin sahihan bayanan dalibai da na jinsinsu tare da adadin wadanda ake kaiwa makaranta babbar matsala ce ga ilimi a kasa baki daya.
Daga cikin wannan tsari tantancewar bayanai da za'a gudanar, za’a dauki bayanan Malamai da matsayin karatunsu da kuma yawan ma’aikatan da basa koyarwa da sauran bayanai.
Ana sa jawabin, Ministan babban birnin tarayya Mallam Muhammad Bello ya ce, Abuja zata baiwa shirin duk wani hadin kai da zasu nema domin samun nasara shirin.
Samar da wannan hanya ta tantance malamai da dalibai da ma’aikatan ilimi da sauran kayayyakin aikin fannin koyo da koyarwa, zai taimaka matuka wajen wayar da kai da kuma sanin irin matakan da ya kamata a dauka domin cigaban sashin ilimin kasar nan. Mr Abdulahi Salifu, Daraktan shiyya na UNESCO ya bayyana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng