Hukumar Navy ta karbe buhunan shinkafa 642 daga hannun masu shigowa da ita ta barauniyar hanya
- Hukumar Navy ta Najeriya a Ibaka dake karamar hukumar Mbo, sunyi nasarar damke mutane takwas masu safara ta barauniyar hanya kuma sun karbe buhuna 642 na shinkafa daga hannunsu
- Mutanen takwas da aka kama duk ‘yan Najeriya ne, wadanda aka kama a hanyarsu ta dawowa Najeriya da kayayyakin ta cikin ruwa ba kan ka’ida ba
- Kwamandan Sojojin FOB, Kaptin Yusuf Idris a ranar Asabar ya gargadi masu sufuri ta barayin hanyoyi dasu kiyayi kansu da shiga yankunan sojojin ruwa na Najeriya
Hukumar sojin ruwa ta Najeriya a Ibaka dake karamar hukumar Mbo, sunyi nasarar damke mutane takwas masu safara ta barauniyar hanya kuma sun karbe buhuna 642 na shinkafa, sai Injina guda hudu, saina injinan ban ruwa biyu sannan sai kananan jiragen ruwa na katako guda biyu daga hannunsu.
Mutanen takwas da aka kama duk ‘yan Najeriya ne, wadanda aka kama a ranar Juma’a, a kan hanyarsu ta dawowa Najeriya daga kasar Cameroon, da kayayyakin ta cikin ruwa ba kan ka’ida ba.
Kwamandan Sojojin FOB, Kaptin Yusuf Idris a ranar Asabar ya gargadi masu sufuri ta barayin hanyoyi dasu kiyayi kansu da shiga yankunan sojojin ruwa na Najeriya.
Lokacin da yake mika wadan ake zargin a hannun jami’an Kwastam na Najeriya (NCS), Idris ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa zasu cigaba da taimakawa hukumar Kwastam wurin magance masu shigowa da kayayyaki ta hanyoyin ruwa ba bisa ka’ida ba.
KU KARANTA KUMA: Bazamu taba yin shugaban kasar da ba zai iya zuwa Amurka ba – Lauretta Onochie
Mataimakin shugaban hukumar ta Kwastam ta Eastern Marine, dake Oron House Station, Auwal Ali, wanda ya wakilci shugaban hukumar ta Kwastam na Port Harcourt, Ajiya Masaya, yayi godiya ga hukumar ta Navy bisa ga irin kokarinta.
A halin da ake ciki Sakataren jagorori a Arewa da kuma kungiyar masu ruwa da tsaki a Arewa Dr. Umar Ardo, ya duba yaga cewa wadanda ke cewa kada Buhari ya tsaya takara a zabe na gaba sun fada masa gaskiya. Saboda haka ya umurce shi da ya sauraresu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng