Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus

Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus

- Rigima tsakanin jami'in Dan sanda da wasu matasa ta jawo asarar rayuwar wani saurayi

- Bayan mutuwar saurayin ne kuma wasu gungun matasa su kayi ramuwar gayya kan dukiyar Dan sandan da suke zargi

Rikicin da ya barke tsakanin wani dan haya da mai gidan da yake hayar jami’in Dan sanda mai suna SP Austin, yayi sanadiyyar mutuwar guda da cikin matasan da suke murnar zagayowar ranar haihuwar yar uwarsu a gidan.

Mai gidan dai ya tambayi yan hayan nasa cikin fushi cewa, a wane dalili zasu yi masa bikin Birthday a gidansa ba tare da izini?

Nan take rikici ya barke tsakanin mai gidan SP Austin da yan hayar sakamakon yunkurin mai gidan na dakatar da shagalin nasu.

Faruwar haka ke da wuya sai SP Austin ya kira yan uwansa yan sanda, ammai sai ya ce musu wasu yan kungiyar asiri ne suka shigo masa gida, ba jimawa ne sai ga yan sanda masu yaki da yan kungiyar asiri sun iso gidan, inda sukai awon gaba da matasan wa da kani zuwa shelkwatar yan sanda dake Edo.

Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus
Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus

Mahaifin matasan Mr Joseph Imarogie, wanda shi ma tsohon Dan sanda ne, ya tabbatar da cewa, an kame yayan nasa biyu ne sanadin suna bikin murnar haihuwar jikarsa ba tare da sun nemi izinin mai gidan da suke haya ba.

Ya kuma kara da, bayan tafiya da su ne ofishin yan sandan aka yi ta gana musu azaba kafin bayar da belin su, amma tuna daya daga cikinsu ya illata.

An dai rawaito cewa bayan bayar da belin su, guda daga cikin matasan ya shiga cikin mawuyacin halin da har sai da aka kai shi asibiti don yi masa magani, kuma acan din ya ce, ga garinku nan.

Rasuwar matashin ce ta hasala yan uwansa yin takanas zuwa gidan, suka kuma cinna masa wuta ya kone kurmus.

KU KARANTA: Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira

Wannan lamari dai duka ya faru ne a unguwar Evbuomama dake karamar hukumar Ikpoba-Okah ta jihar Edon.

A nashi barin, mai gidan hayar ya ce, yayi mutukar mamaki da aka ce an kone gidan nasa.

An kira wa waya da safe a ke fadamin cewa, an garzaya da saurayin zuwa asibiti don duba lafiyarsa, inda acan din ne ya rasu. Daga baya kuma iyali na suka kira ni suke fada min wasu mutane sun cinnawa gidanmu wuta.”

Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus
Kwamacala: Wasu fusatattun samari sun bankawa gidan Dan sanda wuta ya kone kurmus

Kakakin rundunar yan sanda na jihar DSP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan kuma yace ya zuwa yanzu sun damke wasu da ake zargin suna da hannu cikin hayaniyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng