Rikicin Makiyaya: Mutane 8 sun mutu an kuma raunata wasu da yawa a Benue

Rikicin Makiyaya: Mutane 8 sun mutu an kuma raunata wasu da yawa a Benue

- Rikicin Makiyaya da Mutanen Benue yana kara damalmalewa

- Rikicin baya-bayan nan dai yayi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da yawa

Wata sabuwar arangama da ta kaure tsakanin Makiyaya da mazauna garin Agagbe dake karamar hukumar Sengev, Gwer a jihar Benue ta yi sanadiyyar lankwame rayuka 8 tare da kuma jikkata wasu da yawa a daren Asabar din da ta gabata.

Rikicin Makiyaya: Mutane 8 sun mutu an kuma raunata wasu da yawa a Benue
Rikicin Makiyaya: Mutane 8 sun mutu an kuma raunata wasu da yawa a Benue

Majiyarmu dai ta bayyana cewa, lamarin ya faro bayan yunkurin da Makiyayan su kayi na shiga ciki garin domin ciyr da dabbobinsu, yayinda su kuma mutanen suka ki yarda da hakan.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda 30 ke zagaye da asibitin da Dino Melaye ya ke jinya

Kafin faruwar ruguntsimin dai an rawaito cewa, Makiyayan kwanan baya sun aika cewa, suna son shigar da dabbobinsu kauyen domin ciyar da su, amma mutane suka ki basu hadin ki. Ba jimawa ne kum sai Makiyayn suka zo su da yawa don su kutsa kai, nan ma ba’a basu hadin kai ba.

Daganan ne suka sake dawo suka ce wai an kashe musu shanu, amma mutanen garin suka ce su ba wanda ya taba shanun Makiyyan, amma suka dage da cewa tabbas an kashe musu shanu. Wasu sunce suna son suyi amfani da hakan ne wajen samun damar shiga garin.

A daren Asabar ne kuma misalign 11 na dare, Makiyayan suka afkawa na Agagbe suka fara harbi kan mai uwa da wabi sannan suka kona bukkoki da gidajen mutane da dama.

Duk yunkurin majiyarmu na tuntubar mai Magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar ASP Moses Yamu ta wayarsa ta hannu domin tabbatar da faruwar harinya ci tura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel