"Mahaifi na ne ya bar mani gadon bindiga sa " - Wani matshi mai shekaru 25
Wani matashi dan shekaru 25 kacal a duniya da ake zargin gawurtaccen barawo ne ya shaidawa 'yan sanda a jihar Osun cewa shi fa bindigar sa ma mahaifin sa ya bar masa ita gado bayan mutuwar sa.
Kamar dai yadda muka samu, jami'an 'yan sandan sun kama matashin ne a yayin da suke bincikar kayan fasinjoji akan hanyar Osun din zuwa Oyo.
KU KARANTA: Batun tsigewa: Buhari zai san makomar sa ranar Laraba
Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan su ce yanzu haka suna kan bincike ne akan lamarin kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kuliya.
A wani labarin kuma, dubun wani likitan bogi ta cika a jihar Katsina bayan da ya shiga komar yan sanda, wanda ake zargin mai shekaru 38 ya kware a harkar sojan gona da cewa wai shi kwararren likita ne, har ma ya sha yiwa mutane allura da karin jini da ruwa balle kuma bayar da magani.
Yanzu haka dai tuni wanda ake zargin mai suna Joseph Umaru ya amsa laifinsa bayan da ya shiga hannun yan sanda.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng