Babban malamin addini a Najeriya ya caccaki shugaba Buhari game da rashin cika alkawari
Wani babban malamin addinin Kirista a Najeriya kuma shugaban darikar Katolika na shiyyar Sokoto Bishof Matthew Hassan Kuka ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tabbatar da cika alkawurran da ya daukar wa 'yan Najeriya lokacin yakin neman zabe.
Haka ma dai Bishof din ya kuma roki sauran 'yan Najeriya musamman ma masu fada a ji da su yi anfani da damar su wajen samarwa kasar tabbataccen zaman lafiya tare kuma gudun duniya da son tara dukiya.
KU KARANTA: Dalilin da yasa Obasanjo da Babangida ba su son Buhari - Ganduje
Legit.ng ta samu cewa Bishop Kukah din yayi wannan kiran ne a cikin wani sakon bukukuwan Esta da ya fitar domin taya sauran mabiya addinin na kirista murnar zagayowar ranar.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano kuma daya daga cikin manyan magoya bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, Alhaji Abdullahu Umar Ganduje ya bayyana cewa babban dalilin da ya ke zargin shine ya sanya tsaffin shugabannin kasar Najeriya Obasanjo da Babangida basu son shugaba Buhari.
A yayin wata fira da gwamnan yayi da majiyar mu, ya bayyana cewa saboda shugaba Buhari yana da zummar yaki da cin hanci da rashawa shi ya sanya ba su son yayi tazarce.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng