Buhari bai alaka da matasa, ba mamaki don ya ce malalata ne – Atiku

Buhari bai alaka da matasa, ba mamaki don ya ce malalata ne – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice a wani tambaya da akayi masa a birnin Landan.

Alhaji Atiku Abubakar ya yi wannan furuci ne a wani taron da ya halarta a Chatham House da ke kasar Birtaniya inda ya gabatar da jawabi a kan takararsa a 2019.

An yiwa Atiku Abubakar tambaya cewa, Menene martaninka ga maganan Buhari na cewa matasan Najeriya malalata ne? Atiku yace:

“ Ban yi mamakin jawabin da yayi ba saboda shi (Buhari) ba mai daukan ma’aikata bane, bai da kasuwanci, bai da makaranta, saboda haka bai alaka da matasa a makarantu. Saboda haka ba laifinshi bane.”

KU KARANTA: Zan binciki Buhari idan na zama shugaban kasa - Atiku

Legit.ng ta kawo muku rahotn cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, kuma mai neman tsayawa takaran shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2019 ya ce zai gudanar da bincike a kan cinikin makamai da gwamnatin shugaba Buhari take saya.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa a yau Asabar, turakin Adamawan yace an dauki lokaci mai tsawo ana ta artabu da yan kungiyar ta Boko Haram amma har yanzu ba'a kawo karshen matsalar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel