Shugaba Buhari, Saraki, Dogara sun halarci daurin auren diyar SGF Boss Mustapha
Shugaba Muhammadu Buhari; shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki; Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara; da wasu manyan kusoshin gwamnati sun halarci taron dauran diyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a yau Asabar.
Wannan shine taro na farko da shugabannin za su hadu bayan sunyi kokarin tsige shugaban kasa a wannan makon.
An daura wannan aure a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, Abuja.
KU KARANTA: Zan binciki Buhari idan na zama shugaban kasa - Atiku
Daga cikin manyan da suka halarci taron sune babban jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, Sanata Ken Nnamani da wasu gwamnoni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng