Yanzu-yanzu: An sake mumunan harin Bam Maiduguri
An kai wani mumunar harin bakin wake gidajen Jidarri Polo da daren nan a Maiduguri, birnin jihar Borno.
Bana Shettima, wani mazaunin garin ya bayyanawa jaridar Cable da daren nan.
Yace an kai wannan hari ne misalin karfe 9:00 na dare kuma hankulan jama'an garin ya tashe.
"Akwai gawawwaki a gaban gidana yanzu nan da nike muku magana" Yace
Legit.ng ta kawo muku rahoton artabu da ya faru tsakanin jami'an tsaro da yan Boko Haram a daren jiya Alhamis.
KU KARANTA: An gano mai kista duk wani makirci na hare-haren jihar Benuwe
Bayan musayar wuta da awanni, jami'an tsaro sun samu galaba kawar da yan ta'addan. Daga baya kuma akaji tashin Bam.
Hukumar yan sandan jihar Borno ta ce mutane 6 ne suka rasa rayukansu a harin da Boko Haram ta kai Jidari Polo, jiya a garin Maiduguri.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Edet Okon, ya bayyana wannan ne a wani jawabin da ya saki yau Juma’a cewa mutane shidan sun kunshi; mamban Civilian JTF 1, masu farar hula 3, da kuma yan kunar bakin wake mata 2.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng