Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro

Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa anyi cacar baki a tsakanin gwamnonin APC bayan sun taru domin zantawa akan wasu muhimman batutuwa da ya shafi jam’iyyar.

Majiyarmu ta ruwaito cewa gwamnonin sun zanta akan lamarin ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa baki daya, ana cikin zantawan ne taron yayi yayi zafi, har sai da wadanda suka kai zuciya nesa suka shiga tsakanin wasu hasalallun cikin su.

Mutane biyu ne ke takarar shugabancin jam’iyyar na kasa – wato John Odigie-Oyegun wanda wa’adin mulkin sa zai kare a karshen watan Yuli, amma aka sake ba shi damar sake tsayawa takara, da kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Majiya ta ce ana tsakiyar taro ne wanda ba a bar manema labarai sun shiga ba, sai rincimi ya harde a tsakanin gwamnonin kan batun taron gangamin jam’iyyar da za a gudanar nan gaba.

Tsarin da aka dauko na canjen wakilai daga jihohi ne ya sosa ran wasu gwamnoni kamar irin Rochas wanda yace bai amince a tura wakilin jihar Imo ko ina ba.

Jin haka, sai gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi caraf, ya ce Okorocha shirme da bankaura kawai ya ke yi, domin ba abin da zai iya yi, tunda ba shi ne kan gaba da kowa a cikin jam’iyyar APC ba.

Ya ce duk abin da jam’iyya ta gindaya, to ya zauna, babu mai tayar da shi.

Har ya kai ga kalubalantar Okorocha da ya yi duk irin dabancin da ya san zai iya idan ya isa.

Ganin abin ya kai Akeredolu da Okorocha tayar da jijiyar wuya, sai sauran gwamnoni suka yi sauri suka ba su hakuri don kada su kai ga cin kwalar juna.

Can kuma bayan an ci gaba da taro, sai Okorocha ya kara kunno wata wutar, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a zabi Adam Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya.

Ya ce Buhari ya fadi haka a lokacin da suka yi ganawa da shi a ranar Alhamis din, kafin su kai ga shiga taron da suke tattaunawar.

Shi kuma Gwamna El-Rufai, wanda dama ya na cikin gwamnonin da suka ziyarci Buhari a ranar, sai ya yi zambur ya karyata Okorocha.

Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro
Yadda Gwamnonin APC suka kusa ba hammata iska a wurin taro

El-Rufai ya ce abin da aka zartas shi ne shugaba da gwamnoni ba za su bada fifiko kan kowane dan takara ba idan kowanen su ya je kamfen.

Rufe bakin El-Rufai ke da wuya, sai gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya nuna El-Rufai ya ce masa haba Malam, ya za ka yi wa mutane baki-biyu?

Kafin wannan taron, kowa ya hakkake cewa El-Rufai ya na bangaren Oyegunn ne. Shi kan sa Oyegun din ya yi amanna cewa duk lokacin da Buhari ya rufe kofa tare da El-Rufai, to gwamnan na share masa hanya ne a wurin shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa auren yan matan Kannywood ke saurin mutuwa - Bintun Dadin-Kowa

Amma nan take sai Ajimobi ya nuna El-Rufai ya ce ai da shi suka je gidan Oshiomhole ranar Talata da dare. To ya na mamakin yadda ya ke nuna kamar ya na goyon bayan Oyegun a sarari.

Ajimobi ya ce a gaban sa El-Rufai ya yi wa Oshiomhole mubayi’a, kuma ya tabbatar masa da cewa shi zai yi nasara a wurin gangamin taron zabe.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar PDP a kano tayi kira ga 'yan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam'iyyar dasu bi kundin tsarin siyasar jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar na jihar Senator Mas' up El-Jibril Doguwa ya tattauna da manema labarai jim kadan da gama taron da sukayi na wayar da kan 'yan takara akan kamfen din zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Asali: Legit.ng

Online view pixel