Dalilin da yasa auren yan matan Kannywood ke saurin mutuwa - Bintun Dadin-Kowa
- Bintun Dadin-Kowa ta yi sharhi akan dalilin yawan mace-macen yan matan Kannywood
- Ta ce babu matar dake da dadin aure inrin yar fim
- Ta daura laifin yawan mace-macen aurensu akan iyayen miji
“A koda yaushe yan matan dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood na da burin zama lafiya a rayuwar aurensu amma mummunan kallon da jama’a keyi masu ya jefa da dama daga cikinsu a matsaloli a gidaje aurensu” inji Fatima Sa’id Abdullahi.
Fatima wacce aka fi sani da Bintun Dadinkowa a Arewa24, ta bayyana cewa babu macen dake da dadin aure irin yar wasa, amma kallon da ake masu na a fim ya rusa farin cikin dake gidajen aure da dama.
Ta ga laifin iyaye wajen hargitsa al’amuran auren yayansu musamman idan ya shafi yar fim a ciki.
Da take amsa tambayoyi kan dalilin da yasa auren yan fim ke saurin mutuwa, Bintu tace “ya danganta da mutanen da abun ya shafa, wasu lokuta zata ga bayan aure yana sonta itama tana son sa amma idan tafiya yayi tafiya sai a samu wani na daban na shiga harkokin gidansu, yana kawo wa dayan labarai marasa dadi akan abokin zaman sa inda hakan yakan haifar da babban matsala a aurensu.
“Lokuta da dama iyayen miji kan zamo masu haddasa fitina sannan su dunga kintsa munanan maganganu akan sirikan nasu kamar yadda mutane ke way an fim mumunan zato.
“Bayan auren sai kuga wasu da basu son ganin farin ciki sun fara sanya munanan zato a zukatan iyayen sai suce dansu ya fada a mugun hannu. “Ta yaya akayi danki mai tarbiya da kamala ya auri waccan mara tarbiyan wacce ta kasance yar fim” daga nan zai matsaloli zai fara kunno kai bayan kwanaki biyu zuwa uku sai aji auren ya mutu", cewar ta.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Rahma Sadau ta karyata rade-radin zagin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e
Asali: Legit.ng