An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja (hotuna)

An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja (hotuna)

- Anyi jana’izan kakakin gwamnan jihar Sokoto

- Zaa binne Imam Imam a makabartan Gudu dake Abuja, babban birnin Najeriya.

- Ya rasu a ranar Juma’a, 27 ga watan Afrilu sakamakon ciwon huhu

A yanzu haka ana nan ana jana’izan Imam Imam, kakakin gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal a Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa zaa binne Imam a makabartan Gudu dake Abuja bayan sallar jana’iza a masallacin An-Noor a Wuse dake Abuja.

An fara sallan ne da 1pm a ranar Juma’a, 27 ga watan Afrilu, bayan sallar Juma’a.

An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja (hotuna)
Imam Imam ya rasu a ranar Juma'a 27 ga watan Afrilu

Mista Imam wanda yayi karatun jarida a Kaduna Polytechnic, ya fara aiki a matsayin dan jarida a New Nigerian. Daga baya ya koma Thisday, inda ya zamo editan kungiyar siyasa.

An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja (hotuna)
Ya kasance kakakin Gwamna Tambuwal

Ya yi aiki a matsayin maiba tsohon kakakin majalisar wakilai, Aminu Tambuwal shawara, tsaknakin 2011 da 2015. Har zuwa lokacin mutuwarsa, Imam ya kasance kakakin gwamnan jihar Sokoto.

An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja (hotuna)
An binne kakakin Gwamna Tambuwal, Imam Imam a Abuja

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Asali: Legit.ng

Online view pixel