Tsige Buhari: 'Yan majalisar tarayya 5 da suka tseratar da Shugaba Buhari
Kawo yanzu dai a iya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tsallake tarkon batun tsige shi da majalisun tarayyar Najeriya suka fara yi tun a farkon makon nan bisa zargin da suka yi masa na kashe wasu kudaden da suka kai $496 miliyan wajen sayen jiragen yaki ba tare da amincewar majalisun ba.
A wata takardar karin bayani da shugaban kasar ya aikewa majalisar ya bayyana masu cewa yayi gaban kansa ne wajen siyen jiragen yakin saboda yana da tabbacin cewar majalisun za su amince da bukatar ta sa.
KU KARANTA: Za'a kammala gina matatun mai 2 kafin karshen shekara a Najeriya
Legit.ng dai kamar yadda ta saba ta binciko maku 'yan majalisun na tarayya da suka hada da majalisar dattijai da kuma wakilai da suka yi ta tada jijiyoyin waya akan lallai ba zai yiwu a tsige shugaban kasar ba.
Da yawan su dai kamar yadda binciken na mu ya tabbatar yan jam'iyya APC mai mulki ne, kuma ga su kamar haka:
Daga zauren majalisar dattijai akwai
1. Senator Shehu Sani (APC, Kaduna)
2. Senator Abu Ibrahim (APC,Katsina)
3. Bala Ibn Na’Allah (APC, Kebbi)
Daga zauren majalisar wakilai kuma akwai
4. Alhassan Ado Doguwa (APC, Kano)
5. Yakubu Dogara (APC, Bauchi)
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng