Tsige Buhari: 'Yan majalisar tarayya 5 da suka so a tsige Shugaba Buhari

Tsige Buhari: 'Yan majalisar tarayya 5 da suka so a tsige Shugaba Buhari

Kawo yanzu dai a iya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tsallake tarkon batun tsige shi da majalisun tarayyar Najeriya suka fara yi tun a farkon makon nan bisa zargin da suka yi masa na kashe wasu kudade ba tare da amincewar majalisun ba.

A wata takardar karin bayani da shugaban kasar ya aikewa majalisar ya bayyana masu cewa yayi gaban kansa ne wajen siyen jiragen yakin saboda yana da tabbacin cewar majalisun za su amince da bukatar ta sa.

Tsige Buhari: 'Yan majalisar tarayya 5 da suka so a tsige Shugaba Buhari
Tsige Buhari: 'Yan majalisar tarayya 5 da suka so a tsige Shugaba Buhari

KU KARANTA: An kama malamin addini da laifin satar yaro

Legit.ng dai kamar yadda ta saba ta binciko maku 'yan majalisun na tarayya da suka hada da majalisar dattijai da kuma wakilai da suka yi ta tada jijiyoyin waya akan lallai sai an tsige shugaban kasar.

Da yawan su dai kamar yadda binciken na mu ya tabbatar yan jam'iyyar adawa ta PDP ne, kuma ga su kamar haka:

Daga zauren majalisar dattijai akwai

1. Sanata Mathew Uroghide (PDP, Edo)

2. Sanata Chukwuka Utazi (PDP, Enugu)

3. Sanata Sam Anyanwu (PDP, Imo)

Daga zauren majalisar wakilai kuma akwai

4. Femi Gbajabiamila (APC, Lagos)

5. Nicholas Ossai (PDP, Delta)

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng