Mutane 6 ne suka hallaka a artabun Boko Haram da Sojoji jiya a Maiduguri - Hukuma
- Anyi mumumar artabu da yan Boko Haram da yammacin jiya
- Hukumar sojin Najeriya ta ce mutane su kwantar da hankulansu
Hukumar yan sandan jihar Borno ta ce mutane 6 ne suka rasa rayukansu a harin da Boko Haram ta kai Jidari Polo, jiya a garin Maiduguri.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Edet Okon, ya bayyana wannan ne a wani jawabin da ya saki yau Juma’a cewa mutane shidan sun kunshi; mamban Civilian JTF 1, masu farar hula 3, da kuma yan kunar bakin wake mata 2.
Okon ya bayyana cwa jami’an SARS da wasu mutane 7 ne suka jikkata sanadiyar harbe-harbe da kuma tashin Bam.
Okon yace: “ A rana Alhamis, 26 ga watan Afrilu,misalin karfe biyar na yamma, yan Boko Haram sun kan mumunan hari Jidari Polo a Maiduguri kusa da babban kotun tarayya.”
“Yan ta’addan sun yi harbe-harben bindiga kuma sun tayar da bama-bamai. Jami’an tsaro sun samu nasarar kawar da su bayan wani artabu da akayi.”
KU KARANTA: 'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hadari a wani gari dake iyaka da jihar Kebbi
Legit.ng ta kawo muku da yammacin jiya cewa ana wani musayar wuta tsakanin yan Boko Haram da jami’an tsaron Najeriya a Maiduguri.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng