Karshen duniya: Dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas

Karshen duniya: Dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas

Wani yaro mai shekaru 19 a duniya mai suna Friday Oyedele an zarge shi da laifin dirkawa wata 'yar yarinya mai shekaru 13 a duniya wadda aka bukaci a sakaya sunan ta ciki.

Kamar dai yadda muka samu, an dai gurfanar da yaron ne a gaban wata kotun majistare ta garin Ikeja, jihar Legas gaban babbar alkaliyar kotun Uwar gida Sule Amzat.

Karshen duniya: Dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas
Karshen duniya: Dan shekara 19 ya dirkawa 'yar shekara 13 ciki a garin Legas
Asali: UGC

KU KARANTA: Ana kokarin yi wa alqur'ani gyaran fuska a Faransa

Legit.ng ta samu cewa ita kuma da take yanke hukunci, alkaliyar ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda ake zargin har sai ta kammala tuntuba da kuma neman shawara daga na gaba da ita.

Tun farko dai kamar yadda muka samu, dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun cewa wanda ya ke karar ya aikata laifin fyade ne a ranar 11 ga watan Janairun 2018.

A wani labarin kuma, Babbar kotun majistare ta unguwar Mpape dake a garin Abuja, babban birnin tarayya ta bayar da umurnin a cigaba da tsare dan uwan Sanata Dino Melaye mai suna Mista Samuel melaye tare da wasu sauran mutane uku a kurkukun Kuje, garin Abuja.

Kamar dai yadda majiyar mu ta tabbatar, ranar Alhamis ne dai kotun ta bayar da wannan umurnin inda tace a tsare mutanen su hudu har sai ranar Litanin, 30 ga watan Afrilu domin cigaba da zaman shari'ar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel