Gwamnatin jihar Gombe ta amince da sabon tsarin mafi karancin albashi
Gwamnatin jihar Gombe a karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Dankwambo ta amince da dabbaka sabon tsarin mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar na Naira dubu ashirin da takwas musamman ma duba da yanayin yadda tattalin arzikin kasar ta tabarbare.
Wannan matsayar dai da gwamnatin ta cimmawa ta fito ne daga bakin shugaban ma'aikatan jihar sannan kuma shugaban kwamitin dabbaka mafi karancin albashin Alhaji Adamu Haruna Abubakar yayin da kwamitin gwamnatin tarayya na sabon tsarin a shiyyar arewa maso gabas ke ganawa.
KU KARANTA: An gano masu bautar bishiya a Kano
Legit.ng ta samu cewa haka kuma Alhaji Adamu ya kara da cewa indai har gwamnatin tarayya na son jahohi su bi sahun su, to dole ne sai sun gyara hanyar da ake bi wajen kasafta kudaden kasar.
A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya fara yakin neman sake zaben sa a karo na biyu yayin da yake jawabi yau a jihar Bauchi lokacin da yaje ziyarar aiki ta kwana daya tare kuma da kara jaddada wa jama'a muhimmancin yin hakan.
Haka zalika ma dai shugaban ya kuma kara da yiwa dumbin mutanen da suka je tarbar tasa ne cewar gwamnatin sa idan dai har ya zarce to zata maida hankali sosai wajen yaki da rashawa tare da kwato kudaden sata da ke a hannun barayin gwamnati.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng