To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade

To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade

- Ana zaton wauta a makera, EFCC ta gamu da fushin kotu

- sakamakon kin bin umarnin kotu yanzu zata biya wanda ta kama tarar kudi mai yawa

Wata babbar kotu a birnin tarayya dake Abuja ta umarci hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da ta saki tsohon Ministan birinin Abujan Malam Bala Muhammed tare da kuma biyansa tsabar kudi har Naira miliyan biyar.

To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade
To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade

Malam Bala dai yana tsare ne a hukumar ta EFCC tun daga ranar 24 ga watan Oktoba zuwa 29 ga watan Nuwambar shekarar 2016 kafin daga bisa ni kotu ta amince da bayar da shi beli.

Amma sai dai hukumar tya EFCC ta bijirewa umarnin kotun, ta cigabada tsare shi har zuwa 29 ga watan Nuwambar 2016.

KU KARANTA: Ana wata ga wata: Gwamnatin jihar Kaduna ta maka El-Zakzaky a kotu bisa wasu caji takwas

A dalilin hakan ne, tsohon ministan birnin tarayyar ya kai humakar ta EFCC kara a ranar 16 ga watan Nuwamba 2016, domin ta tauye masa hakkinsa na walwala, gaban mai shari’a Hussein Baba-Yusuf domin kwatar hakkinsa.

Sai dai ana ta bangaren, EFCC ta ce ta cigaba da tsare shi ne a bisa wani korafi da wani Mutum ya kai mata.

To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade
To fa! EFCC ta tafka asara a kotu, zata biya tarar Miliyoyin kudade

A karshe mai shari’a Baba-Yusuf, ya amince da korafin nasa kana kuma yace, cigaba da tsare Bala Muhammed din ya saba ka’idar kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma an tauye masa hakkinsa.

Sannan kuma ya umarci hukumar da ta biya Bala Muhammad din diyyar kudi har Naira miliyan biyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel