Gwamnatin Najeriya ta bayar da lasisin a fara sayar da maganin cutar sikila
- Cutar sikila dai bakaken fata kadai ke yinta duk duniya
- A hasashen masana, watakil ta faro ne don ta yaki cutar malariya miliyoyin shekaru da suka wuce tun muna birrai
- An bada lasisin a fara hada maganin yakar ta, saboda yadda take azabtarwa
Federal Executive Council (FEC), watau majalisar kasa, ta yarje ma National Institute for Pharmaceutical Research and development (NAPRED) da kuma May and Baker Plc da su fara cinikayya da siyarda Niprisan, maganin cutar sikila a Najeriya.
Ministan lafiya, Isaac Adewole ya bayyana hakan a ranar laraba yayin jawabin da yayi ma manema labarai a karshen taron FEC, wanda aka gudanar a cikin fadar shugaban kasa.
Mista Adewole yace an basu lasisin hada magunguna don kasuwancinsu domin a rage nauyin cutar a Afirka da ma sauran sassa na duniya inda aka fi samun cutar.
Mista Adewole yace cutar sikila ta zama matsala gama gari a cikin bakaken Afirka, kudu maso gabashin Asia da kuma Latin America.
Anyi ittifakin cewa kusan kashi 25 cikin dari na 'yan Najeriya na dauke da kwayar halittar cutar da sama da miliyan biyu suna dauke da cutar.
Kamar yanda Adewole yace, an fara amfani da maganin ne a jihar Oyo sama da shekaru 20 da suka wuce kuma NAPRED tayi bincike don tabbatar da ingancin maganin kuma an basu lasisi.
DUBA WANNAN: Dubi yawan masu mika wa gwamnati bayanan sirri kan kudaden sata
"Muna so ne mu farfado da maganin kuma a dinga siyar da shi a Najeriya. Munsan cewa hada maganin da siyarda shi a Najeriya zai kawo sassauci ga miliyoyin 'yan Najeriya masu cutar." yace.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng