Dalilin da ya sa bamu sa baki a al’amarin yan Shi’a – Kungiyar MURIC

Dalilin da ya sa bamu sa baki a al’amarin yan Shi’a – Kungiyar MURIC

Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta saki jawabi inda tayi bayanin dalilin da yasa batayi wani furuci kan rikicin da ke faruwa tsakanin jami’an yan sanda da yan Shi’a kan cigaba da rike shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

Kungiyar wacce ke da hakkin dukkan Musulmai a Najeriya ta ce ba zata iya cewa komai akan abubuwan da yan Shi’a keyi ba saboda dalilai da ya kunshi kishin kasa.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan jawabi ne a matsayin martini ga maganan sakataren kungiyar Shi’a, Abdulmumin Giwa, inda ya soki kungiyoyin kare hakkin addini kan banza da su duk da halin da suke ciki da cin mutuncin da gwamnati ke musu.

KU KURANTA: Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta saka wa Ofishin yakin neman zaben Buhari jan fenti

A makon da gabata, mambobin kungiyar Shi’a sun yi fito-na-fito da jami’an yan sanda a Abuja yayinda suke zanga-zanga kan cigaba da tsare shugabansu, Sheik Al-Zakzaky, wanda aka kama a Disamban 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng