Gwamnoni Najeriya sun hadu domin tattauna yadda zasu karbi ragowar kudin Paris Club

Gwamnoni Najeriya sun hadu domin tattauna yadda zasu karbi ragowar kudin Paris Club

- Gwamnoni zasu dara nan gaba kadan

- Za'a kara sakar musu karin wasu kudaden na Paris Club

Gwamnonin jahohi 36 ne na fadin kasar nan suka hadu a babban birnin tarayya Abuja a jiya Laraba karkashin inuwar kungiyar gwamnoni ta kasa, domin tattaunawa kan yadda zasu karbi kashi na karshe na kudin Paris Club.

Gwamnoni Najeriya sun hadu domin tattauna yadda zasu karbi ragowar kudin Paris Club
Gwamnoni Najeriya sun hadu domin tattauna yadda zasu karbi ragowar kudin Paris Club

Kudin dai na Paris Club, kudi ne da gwamnatin tarayyar ta yayyanke a asusun jahohin da ya zarce ka’idar abinda ya kamata domin biyan bashin da Najeriya ta ci daga shekarar 1995 zuwa 2002.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne dai ya biya kashin farko na kudin ga jahohn, kimanin biliyan N388 ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2016.

Haka zalika an sake biyan kudin a watan Yuli na 2017 da ya kai biliyan N134.44, wanda ya kai jimillar kudin har biliyan N522.74.

Har ila yau, a watan Disambar 2017 gwamnati ta sake biyan gwamnonin Naira biliyan N243.79.

KU KARANTA: Dan sanda mai neman na goro ya kashe dan achaba a jihar Ebonyi

A watan Oktobar shekara da ya gabata ne wasu gwamnoni 6 suka gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari a madadin ragowar gwamnoni domin isar masa da bukatarsu ta a biya su ragowar kudaden na Paris Club don su yi amfani da su wajen aiyukan raya kasa.

A yayin haduwar tasu, gwamnonin zasu tattauna batun samar da zauren kasuwanci na Nahiyar Africa don masu zuba jari da hasashen saukar ruwan sama domin damunar bana da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng