An gudu ba’a tsira ba: Yan bindiga sun hallaka wasu yan gudun hijira guda 7 a sansani
Wasu gungun yan bindiga sun da ake zargin makiyaya ne sun hallaka wasu yan gudun hijira guda bakwai a sansaninsu dake karamar hukumar Awe na jihar Nassarawa, inji rahoton The Cables.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar matasan kabilar Tibi na jihar Nassarawa, Peter Ahemba ya tabbatar da haka a ranar Laraba 25 ga watan Afrilu, inda yace yan bindigar sun yi kwantan bauna ne a kan hanyar da yan gudun hijiran ke zuwa daukan kayan abinci.
KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Kotu ta garkame Sanatan Najeriya ya Kurukukun jihar Legas
A yanzu haka dai yan kauyen da sansanin yake sun tarwatse, kowa ya kama gabansa don gudun dawowar yan bindigar, sai dai Ahemba ya bukaci yan kabilar Tibi da su kara hakuri, kuma su kwantar da hankulansu, don sun mika rahoton harin ga hukumar da ta dace.
“A matsayinmu na yan kabilar Tibi yan asalin jihar Nassarawa bamu da wajen zuwa mu tsira, don haka muke kira ga gwamnanmu Tanko Almakura ya kawo mana dauki, mun yaba da kokarin da hukumomin gwamnati ke yi, amma zamu cigaba da raki har ai dawwamammen zaman lafiya ya samu.” Inji shi.
Shi ma Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Kennedy Idrisu ya bayyana cewar rundunarsu bata samu wannan rahoton harin ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng